Isa ga babban shafi
Iran-Turai

Iran za ta iya maida martani mai zafi kan takunkuman Amurka

A daidai lokacin da ake gaf da cika shekara daya da ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta kulla da kasashen duniya, abu ne mai yiyuwa Iran ta mayar da martani dangane da wannan mataki, kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar ya ruwaito.

Shugaban Iran Hassan Rouhani.
Shugaban Iran Hassan Rouhani. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Iran dai ta jima tana barazanar daukar mataki akan Amurka, bayan da Donald Trump ya sanar da ficewar Amurka daga yarjejeniyar, sai dai barazanar ta Iran ta sake bijirowa ne sakamakon sabbin takunkumai da ke hana sayen man kasar da Amurka ta sake kakaba wa kasar, da suka fara aiki a farkon wannan wata.

A ranar 8 ga watan Mayun shekarar bara Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran, kafin daga bisani Amurkan ta ci gaba da sanya takunkumai kan kasar ta Iran.

Yarjejeniyar wadda aka sanya wa hannu a shekara ta 2015, ta samu amincewar manyan kasashe da suka hada da ita kanta Amurka, Rasha, Faransa, Birtaniya. China da kuma Jamus, to sai dai bayan zuwansa kan karagar mulki Donald Trump ya bayyana cewa tana tattare da kura-kurai.

A karkashin sashi na 26 da kuma na 36 na wannan yarjejeniya, Iran na da hurumin ficewa daga yarjejeniyar matukar Amurka ko kuma daya daga cikin wadannan kasashen 6 ya ki cirewa kasar takunkuman karya tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.