Isa ga babban shafi
Iraq-IS

Iraqi ta fara shari'ar wasu mayakan IS 'yan kasashen Ketare 900

Wata kotu ta musamman da ke shari’ar wadanda ake zargi da aikata laifukan ta’addanci a Iraqi ta fara shari’ar mayakan ISIS ‘yan kasashen ketare 900 da suka tsere daga Syria bayan farmakar maboyarsu ta karshe da dakarun sojin Syria suka yi cikin watan jiya.

Firaministan Iraqi Adel Abdel Mahdi
Firaministan Iraqi Adel Abdel Mahdi Iraqi Parliament Office/Handout via REUTERS
Talla

Tun bayan farmakar maboyar karshe ta mayakan na ISIS a Syria ne, dakarun SDF da ke samun goyon bayan Amurka a Syrian suka mika tarin mayakan dukkaninsu ‘yan kasashen ketare, ga mahukuntan Iraqi lokacin da su ke kokarin tserewa.

Wata majiya daga kotun wadda ta yi shura wajen yanke hukunci kan laifukan ta’addanci, ta ce za a rarraba zaman shari’ar mayakan su 900 ne zuwa rukuni-rukuni don zartas musu da hukunci.

Iraqi wadda tun tuni ta hukuntan wasu tarin ‘yan kasar da ta samu da hannu a kungiyar ta IS, da kan ta, ta bukaci kasashen duniya su biya ta dala miliyan 2 kan kowanne mayaki daya duk shekara don hukunta shi a kasar, ko kuma ta sake su su koma kasashensu.

A shekarar da ta gabata ta 2018, dai Iraqin ta yankewa mayakan ISIS akalla 125 hukuncin kisa sama da 65 da ta yankewa hukuncin a 2017, duk kuwa da ikirarin kungiyar Amnesty International na cewa an samu raguwar yanke hukuncin kisar a duniya.

Mayakan na ISIS 900 da suka fito daga kasashen duniya 52 kari ne akan wasu tarin mayakan na ISIS ‘yan kasashen ketare da yanzu haka ke tare a hannun Iraqin ciki har da Faransawa 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.