Isa ga babban shafi
India-Pakistan

Sabon fada ya barke tsakanin India da Pakistan

Fada ya sake barkewa tsakanin India da Pakistan a daren jiya zuwa yau Asabar a yankin Kashmir, wanda ya yi sanadin hallakar jimillar fararen hula 5 da sojoji 2 daga bangarorin kasashen.

Wasu sojojin Pakistan a inda suka kakkabo jirgin yakin India da ya ketara kan iyakarsu da ke yankin Kashmir.
Wasu sojojin Pakistan a inda suka kakkabo jirgin yakin India da ya ketara kan iyakarsu da ke yankin Kashmir. STR/AFP/Getty Images
Talla

Tsohuwar gaba tsakanin kasashen 2 ta sake zafafa ne a karshen Fabarairu da ya gabata, bayan da jiragen yakin India, suka kai farmaki kan wani yankin Pakistan da ke kan iyakarsu, inda Indian ta ce sansani ne na wasu ‘yan ta’adda da ke shirin kaddamar da hare-hare akanta.

India ta kai farmakin ne makwanni kalilan, bayan da a farkon watan na Fabarairu kungiyar da ke kiran kanta da J.E.M. ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da ya hallaka sojin India 40, a yankin Kashmir da ke karkashin ikonta.

Tun a shekarar 1989, kungiyoyin ‘yan tawaye ke yakar mulkin India a yankin Kashmir, inda suke faftukar ganin mayar da ilahirin yankin a karkashin ikon Pakistan, ko kuma a bashi damar zama kasa mai cin gashin kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.