Isa ga babban shafi
Afghanistan

Sama da mutane dubu 30 sun hallaka a yakin Afghanistan

Majalisar dinkin duniya, ta ce hasarar rayukan fararen hula da aka samu a yakin Afghanistan cikin shekarar 2018, shi ne mafi muni, a shekaru kusan 20 da aka shafe ana gwabza yaki tsakanin dakarun Amurka da mayakan Taliban.

Wasu 'yan kasar Afghanistan yayin jana'izar fararen hular da suka rasa rayukansu a yakin kasar.
Wasu 'yan kasar Afghanistan yayin jana'izar fararen hular da suka rasa rayukansu a yakin kasar. AP/File
Talla

Rahoton da aka wallafa a jiya Lahadi, ya nuna cewa an samu karin kashi 11 cikin 100 na fararen hular da suka hallaka a kasar ta Afghanistan da yawansu ya kai dubu da 804, wasu dubu 7 da 189 kuma suka jikkata, idan aka kwatanta da adadin shekarar 2017.

A shekarar ta 2018 kadai, hare-haren kunar bakin wake sau 65 aka kai a sassan Afghanistan, mafi akasarinsu a babban birnin kasar Kabul, inda hare-haren suka yi sanadin mutuwar sama da fararen hula dubu 2 da 200.

A gefe guda kuma rahoton ya ce, hare-haren hadin gwiwa na jiragen yakin Amurka da sojin kasar sun hallaka mutane 500 a shekarar ta 2018.

Rahoton, ya zo ne dai dai lokacin da ake sa ran a yau wakilan Amurka, da na kungiyar Taliban za su gana a Doha babban birnin kasar Qatar don kawo karshen yakin da suke gwabzawa.

A cewar Majalisar dinkin duniya, a cikin shekaru 10 da suka gabata kadai, fararen hula dubu 32,000 suka hallaka a yakin Afghanistan, wasu akalla dubu 60 kuma suka jikkata.

A halin da ake ciki shugaban Amurka Donald Trump ya dukufa wajen kawo karshen yakin da Amurka ta ke yi da al-Qa’eda, Taliban da kuma ISIS a kasar ta Afghanistan, inda yake fatan janye dakarun Amurkan dubu 14 da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.