Isa ga babban shafi
China-Taiwan

China zata afkawa Taiwan

Shugaban China Xi Jinping a fusace ya gargadi hukumomin Taiwan da su sake manufa tareda mika wuya zuwa kasar China don kasancewa kasa daya.

Xi Jinping Shugaban kasar China
Xi Jinping Shugaban kasar China AFP/POOL/Mark Schiefelbein
Talla

Shugaban China a yayinda yake ganawa da membobin gwamnatin China ya jaddada cewa indan ta kama China zata yi amfani da karfin soji wajen sake dawo da Taiwan karkashin ikon ta.

A shekara ta 2017 dai ne shugabannin kasashen China da Taiwan suka gana da juna a karon farko tun yakin basasa da ya raba kasashen biyu, shekaru sama da 67. Shugaban China XI Jinping da takwaransa na Taiwan Ma Ying-jeou sun gama hannu na tsawon sama da minti guda, ala’amarin da ba a zaci zai faru ba a haduwar shugabannin biyu.

Shugabannin sun yi murmushi a lokacin da suke gaisawa da juna a gaban ‘yan jaridu.

Wannan dai ne karon farko da Shugabannin bangarorin biyu suka hadu tun ballewar Taiwan daga China a 1949.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.