Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Mutanen 68 sun mutu a harin ta'addancin Afghanistan

Hukumomi a Kasar Afghanistan sun ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin kunar bakin wanke da aka kai kan masu zanga zanga a jiya talata ya kai 68, a yayin da kasar ke cigaba da samun karuwar tashin hankali.Ataullah Khogyani, mai Magana da yawun gwamnan Nangahar ya ce, mutane 165 ne suka jikkata wadanda a halin yanzu ke karbar magani a asibitoci.

Harin kunar bakin wake a  birnin Kabul kan cibiyar Ilimi ta  Mahdi Mooud
Harin kunar bakin wake a birnin Kabul kan cibiyar Ilimi ta Mahdi Mooud DR
Talla

Wannan harin kunar bakin wake dai, an kai shi ne kan masu zanga zangar adawa da nada shugaban Yan Sanda a Yankin ne.

kasar Afghanistan ta sake tsintar kanta cikin wani sabon yanayin kara tabarbarewar lamaruna tsaronta, tun bayan sake yinkurowar da kungiyoyin Taliban da na Isis suka yi a farkon wannan shekara, al’amarin da ke ci gaba da haddasa hasarar rayuka da kuma zubarda jinin al’ummar kasar.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dau nauyin harin kunar bakin waken na jiya talata, a yankin da kungiyoyin yan ta’adda Isis da Taliban ke gudanar da ayukansu. Duk kuwa da cewa, mafiya yawan hare haren kunar bakin waken da suka wakanan a baya bayan nan kungiyar Isis ce ke daukar alhakin kai su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.