Shugaban kungiyar ISIS ya fitar da sabon bidiyo
Karo na farko a cikin watanni 11, jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ya fitar da sako na farko zuwa ga mabiyansa, inda ya ke jinjina musu dangane da abin da ya kira ci gaba da tunkarar makiya kuma abokan hamayya.
Wallafawa ranar:
Sakon wanda aka fitar jiya Laraba, ya tabbatar da cewa Al-Baghdadi na nan a raye, sabanin rahoton da ya bulla a baya, wanda cikinsa dakarun kawance karkashen jagorancin Amurka suka yi ikirarin kashe shi a wani farmaki da suka kai kan maboyarsa da ke kasar Iraki.
Karo na farko kenan da al-Baghdadi ya fitar da sako na faifan bidiyo tun bayan na karshe ya fitar a cikin watan Satumba a shekarar 2017 da ta gabata.
Har yanzu dai ba’a kai ga tantance ainahin lokacin da aka dauki hoton bidiyon na baya bayan nan ba, sai dai daga cikin jawabin da ya gabatar al-Baghdadi, ya yi tur da alkawarin da kasar Saudiya ta yi, na bayar da tallafin dala miliyan 100, domin sake gina Syria, musamman yankin arewa maso gabashin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu