Isa ga babban shafi
Pakistan

Khan ya kama hanyar zama Firaministan Pakistan

Jam'iyyar da ke mulkin Pakistan ta ki amincewa da sakamakon farko na zaben da aka gudanar da ke nuna tsohon tauraron kwallon kiriket, Imran Khan ya kama hanyar zama sabon Firaministan kasar.

Imran Khan na jawabi ga dandazon magoya bayansa a Pakistan
Imran Khan na jawabi ga dandazon magoya bayansa a Pakistan REUTERS/Stringer
Talla

Shugaban Jam’iyyar Muslim League-Nawaz da ke mulkin Pakistan, Shahbaz Sharif ya yi watsi da sakamakon farko da aka fara bayyanawa a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da kidayar kuri’u.

Yayin ganawa da manema labarai a Lahore, Sharif ya ce, abin da suka gani na magudi ya mayar da Pakistan shekaru 30 baya, saboda haka sun ki amincewa da sakamakon.

Shi ma shugaban Jam’iyyar PPP, Bilawal Bhutto Zardari ya aike da sako ta Twitter da ke cewar 'yan takarar jam’iyyarsa na korafi kan cewa an kori wakilansu a tashoshin kidayar kuri’u, yayin da Jam’iyyar PML-N ta yi zargin cewa, jami’an tsaro sun karbe iko da tashoshin zaben.

Sardar Muhammad Raza, shugaban hukumar zabe ya ce, an samu kashi 100 na adalci wajen gudanar da zaben.

Tuni magoya bayan Imran Khan suka fara bukukuwan murna saboda yadda sakamakon ya nuna shi a matsayin wanda ke kan gaba wajen lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.