Isa ga babban shafi

Faransa ta aike da kayan agaji ga fararen hular Syria

Faransa ta aike da agajin magunguna da yawansu ya kai ton 50 zuwa yankin gabashin Ghouta da ke Syria, bayan samun amincewar Rasha wajen isar da agajin ga fararen hula.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin ganawa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a birnin Moscow, 15 ga watan Yuli, 2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin ganawa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a birnin Moscow, 15 ga watan Yuli, 2018. Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS
Talla

Agajin wanda ake sa ran isarsa zuwa sansanin sojin Rasha da ke arewa maso yammacin Syria a yau Asabar, ya zo sakamakon cimma matsaya tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron, da takwaransa na Rasha Vladmir Putin, bayan daukar lokaci suna tattaunawa akan batun, tun a watan Mayu da ya gabata.

Faransa na fatan taimakawa mutane 500 da ke cikin halin jikkata sosai, yayinda za ta taimakawa wasu masu fama da kananan cutuka akalla 15,000 a kasar ta Syria.

Faransa ta zama kasar turai ta farko kenan da ta fara aikewa da kayayyakin agaji ga fararen hular Syria, tun bayan barkewar yakin kasar.

Majalisar dinkin duniya ta ce bayan shafe tsawon lokaci a karkashin kawanyar dakarun Syria, fararen hula dubu 25 ne kawai daga cikin akalla 500,000 suka samu agajin kayayyakin abinci da magunguna a yankin na gabashin Ghouta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.