Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mayakan Taliban sun hallaka sojin Afghanistan 30

Mayakan kungiyar Taliban sun hallaka sojojin kasar Afghanistan 30, tare da kame wani sansanin soja daya, a lardin badghis da ke yammacin kasar, a wani hari da ta kai wa dakarun kasar a yau Laraba.

Mayakan Taliban sun kai hari na farko bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Mayakan Taliban sun kai hari na farko bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta. AP
Talla

Harin da kungiyar ta Taliban ta kai, shi ne na farko tun bayan karewar wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar da ta sanar tsakaninta da dakarun kasar gabannin ranar Sallah karama, tsawon kwanaki 3, wadda ta kare a ranar Lahadi.

Abdul Azizi Bek, babban jami’i a gwamnatin lardin Badghis, ya ce mayakan na masu yawan gaske ne suka yi ta bullowa daga sassa daban, a lokacin da suka kai farmakin na baya bayan nan.

A cewar jami’an sojoji sun hallaka mayakan Taliban akalla 15 a lokacin da suka shafe sa’o’i kimanin biyu suna gwabza fada.

Ana kyautata zaton cewa mayakan na Taliban sun yi amfani da damar da suka samu ce, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ke aiki a lokacin murnar Sallah, wajen nazarin sansanin sojin da suka kai wa hari.

A ranar Lahadi da ta gabata kungiyar Taliban ta yi watsi da tayin kara wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar da ta sanar tsakaninta da dakarun Afghanistan, domin bai wa ‘yan kasar damar hutun Sallah cikin kwanciyar hankali.

Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce, da zarar yarjejeniyar ta ta kare a daren ranar ta Lahadi, za ta ci gaba da kai wa sojin kasar hare-hare.

A ranar Asabar da ta gabata, shugaban Afghanistan Ashraf Gani ya roki kungiyar ta Taliban, ta bi sawun matakin da ya dauka na tsawaita wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar da suka sanar gabannin ranar Salla, abinda ya baiwa mayakan damar shiga cikin biranen kasar tare da gaisawa cikin raha da sojin kasar da fararen hula cikin raha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.