Isa ga babban shafi

Trump da Kim Jong-un sun hallara a Singapore

Shugaba Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un, sun hallara a kasar Singapore, domin ganawa, irinta ta farko a tarihin bangarorin biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da ya sauka a kasar Singapore, ranar Lahadi, 10, ga watan Yuni, 2018.
Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da ya sauka a kasar Singapore, ranar Lahadi, 10, ga watan Yuni, 2018. Reuters/Jonathan Ernst
Talla

Babban makasudin ganawar da za ta gudana a ranar Talata, mai zuwa shi ne batun shirin mallakar makaman nukiliyar Korea ta Arewa, da Amurka ke neman ta yi watsi da shin a din din din.

Tun bayan gabar da ta kullu a tsakanin kasashen biyu bayan yakin Korea na sjekarun 1950 zuwa 1953, shugabannin kasashen biyu basu taba tattaunawa ba ta kai tsaye ko kuma ta wayar tarho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.