Falasdinawa sun kaddamar da gangami akan iyakar Isra'ila
Daruruwan Falasdinawa a yankin Gaza sun kafa tantuna akan iyakar yankin da Isra’ila, yayin shirin kaddamar da gagarumin gangami na nuna bacin ransu kan Isra’ila, na tsahon makonni 6.
Wallafawa ranar:
Sai dai kuma ana fargabar komai ka iya faruwa tsakanin su da Sojin Isra’ila da suka ja daga
Falasdiwan da ke samun goyon bayan kungiyar Hamas, na cigaba da tsayawa kai da fata wajen kafa tantunan, a dai dai lokacin da ake cigaba kallon kallo, tsakanin su da sojin Isra’ila
Koda yake dai masu shirya gangamin sun ce na lumana ne, Isra’ila tace akwai fargabar fakewa ne da guzuma don harbin karsana.
Kawo yanzu dai Falasdinawa biyar aka harbe, yayinda suka hari iyakar Isra’ila, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Falsdinun ta tabbatar.
Lamarin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka ke kokarin tabbatar da ofishin jakadancinta a birnin Kudus, abinda Palasdinawan suka bayyana da ranar masifa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu