Fasinjojin jirgin Iran 66 sun hallaka
Jami’an agaji sun ce baki dayan mutane 66 da ke cikin wani jirgin saman Iran da ya yi hadari sun hallaka.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jirgin saman fasinjan ya yi hadari ne a wani yankin tsakiyar kasar mai cike da tsaunuka, da ke gaf da garin Semirom sakamakon rashin kyawun yanayi.
Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa birnin Yasuj dake kudu maso yammacin kasar daga birnin Teheran dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata 6, a lokacin da hadarin ya auku.
Jirage masu saukar ungulu dauke da jami'an agaji, sun gaza kaiwa inda jirgin ya yi hadari sakamakon yawaitar hazo, abin da ya tilas ta musu kokarin, ceto ta kasa duk da suna fuskantar matsalar dusan kankara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu