Isa ga babban shafi

Trump ya gindaya wa'adin sake fasalta yarjejeniyar nukiliyar Iran

Shugaban Amurka Donald Trump, ya amince da ci gaba da daga wa Iran kafa, dangane da ci gaba da wanzuwar kasarsa cikin yarjejeniya kan shirin nukiliyar da aka cimma tsakanin kasar ta Iran da kuma manyan kasashen turai.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Sai dai Trump ya yi gargadin cewa tilas sauran kasashen turai su bashi hadin kai, wajen gyara kurakuran ta ke tattare da yarjejeniyar nukiliyar ta Iran, ko kuma su fuskanci ficewar Amurka daga cikinta.

Trump ya jaddada cewa wannan shi ne karo na karshe da zai daga wa kasar ta Iran kafa, kan kaucewa sake kakaba mata takunkuman, kuma tilas a bi sabbin sharuddan da zai gindaya kan yarjejeniyar, wadda aka cimma domin hana Iran mallakar makamin nukiliya, cikin wa’adin watanni 4.

Kungiyar tarayyar turau EU, ta ce ta fara nazari kan kalamai da kuma matasayar ta shugaban na Amurka kan yarjejeniyar domin tantance amfani ko akasinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.