Isa ga babban shafi
Thailand

Kotu ta yankewa matashi hukuncin shekaru 13,000 a kurkuku

Wata kotu a kasar Thailand ta yankewa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru dubu 13,000, bayan samunsa da laifin damfarar mutane miliyoyin daloli.

Wani matashi a Thailand ya yi nasarar damfarar dubban mutane.
Wani matashi a Thailand ya yi nasarar damfarar dubban mutane. stuff.co.nz
Talla

Matashin dan shekara 34, mai suna Pudit Kitti-Thradilok, ya amince da yaudarar dubban mutane da wani shirinsa na bogi da ya kirkira, domin juya kudade don sama musu riba mai tsoka.

Hakan yasa akalla kimanin mutane dubu 40,000 suka zuba kudaden da yawansu ya zarta dala miliyan 160 cikin asusunsa.

Bayan sauraron shari’ar ce, kotu ta samu Kitti-Thradilok da laifuka, dubu 2,653 dukkanin su kan damfara, to sai dai sakamakon amsa laifinsa ba tare da shari’a ba, kotu ta rage shekarun zaman da zai yi a gidan yari zuwa dubu 6, 637, a maimakon dubu 13,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.