Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiyya

Saudiyya ta jefa milyoyin mutanen Yemen cikin yunwa

Malaisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar duniya za ta fuskancin bala’in yunwar da ba’a taba gani ba, sakamakon kawanyar da Saudiyya da kawayen ta su ka yi wa Yemen sannan kuma suka hana kungiyoyin agaji kai wa jama’ar kasar kayan agaji.

Wadanda yunwa ta kama kwance a asibitin Sanaa da ke Yémen, ranar 27 Yulin 2017
Wadanda yunwa ta kama kwance a asibitin Sanaa da ke Yémen, ranar 27 Yulin 2017 REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Mark Lowcock, mataimakin Babban Magatakarda na Majalisar Dinkin Duniyar mai kula da ayyukan jinkai, ya ce rashin daukar matakin da ya dace na iya sanadiyyar ajalin rayukan miliyoyin mutanen da tuni suka tagayyara.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya tattauna da Ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir wanda ya ce za su yi nazarin bukatar Majalisar wadda ta shafi bayar da damar isar da kayan agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.