Isa ga babban shafi
Myanmar

Suu Kyi ta kai ziyarar farko zuwa Rakhine

A karon farko jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, ta ziyarci Jihar Rakhine domin ganewa idanta halin da ake ciki, bayan kisan kare dangin da aka yi wa ‘yan kabilar Rohingya Musulmi da kuma tilastawa dubbai tserewa zuwa kasar Bangladesh domin samun mafaka.

Jagorar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi tare da mukarrabanta.
Jagorar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi tare da mukarrabanta. REUTERS/Stringer
Talla

Kakakin Gwamnatin kasar Zaw Htay yace cikin rangadin na kwana guda, Suu Kyi zata ziyarci yankunan Maungdaw da Buthiduang, inda rikicin yafi muni.

Sai dai babu wani Karin bayani kan ko Suu Kyi zata ziyarci sauran kauyukan da sojin kasar ta Myanmmar suka kone tare da goyon bayan wasu mabiya addinin Buddha da ake zargin sune suka fara farma kauyukan ‘yan kabilar ta Rohingya Musulmi.

Akalla Yan kabilar Rohingya 600,000 aka bayyana cewar yanzu haka suna cikin Bangladesh, kuma ko a jiya an ruwaito cewar karin 2,000 sun sake tserewa zuwa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.