MDD za ta yi taro na musamman kan Myanmar
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taro na musamman gobe juma’a domin sauraron tsohon Sakatare Janar Kofi Annan kan halin da 'Yan kabilar Rohingya a Myanmar ke ciki.
Wallafawa ranar:
Kasashen Faransa da Burtaniya suka bukaci gudanar da taron da Annan yayin da Majalisar ke nazari kan irin matakan zai dauka nan gaba domin magance matsalar.
Hukumar kare hakkin Bil'Adama ta Majalisar ta ce sojojin Myanmar sun kaddamar da hare-hare ne domin raba 'Yan kabilar Rohingya Musulmi da Jihar Rakhine.
Kungiyar kasashen Turai na shirin katse duk wata hulda da kasar ta Myanmar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu