Isa ga babban shafi
Iraqi

Iraqi ta sanar da kwato Hawija

Firaministan Iraqi Haidar Al-abadi, ya ce dakarun kasar sun yi nasarar kwace garin Hawija da ke kusa da iyakar kasar da Syria daga hannun mayakan kungiyar IS.

Dakarun Iraqi suna murnar kwato Hawija
Dakarun Iraqi suna murnar kwato Hawija REUTERS/Stringer
Talla

A cewar mahukuntan kasar, Hawija shi ne gari na karshe a hannun mayakan na IS bayan da aka fatattake su daga Mosul da kuma Anbar.

Al Abadi ya ce yanzu abin da ya rage shi ne kwato sauran yankunan Iraqi da ke kan iyaka da Syria.

An nuna dakarun Iraqi a Talabijin suna murna a lokacin da suke shiga garin Hawija da suka kwato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.