Afghanistan
NATO ta ce Amurka ta jikkata mutane a Kabul
Kungiyar Kawancen tsaro ta NATO ta ce wasu jerin hare-haren saman da Amurka ta kai Kabul da ke Afghanistan sun yi sanadiyar jikkata mutane da dama.
Wallafawa ranar:
Talla
Sanarwar da kungiyar ta bayar ya nuna cewar an kai hare-haren ne kan wasu mutane da ake zargin 'yan ta’adda ne lokacin da suka harba makamin roka jin kadan bayan saukar Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis a Kabul.
Ma’aikatar cikin gidan Afghanistan ta ce mutun guda ya mutu yayin da 11 suka jikkata.
Kungiyar Taliban da mayakan ISIS sun dauki alhakin harba makamin rokar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu