Isa ga babban shafi
Saudiya

Mata za su fara halartar bukukuwan ranar 'yanci a Saudiya

Karon farko a tarihi Sa’udiyya, ta amince da gayyatar mata don halartar bukukuwan ranar ‘yanci wanda aka saba gudanarwa kowacce shekara a filin wasanni na Sarki Fahad. Yanzu haka dai bikin ranar ‘yancin karo na 87 da zai gudana zai samu halartar iyalai inda kuma za a ware guraren zaman maza da kuma wurin da yara dama mata za su zauna.

Daruruwan mata ne dai yanzu haka ke shirin halartar bikin na ranar 'yanci karon farko a Saudiya.
Daruruwan mata ne dai yanzu haka ke shirin halartar bikin na ranar 'yanci karon farko a Saudiya. Reuters
Talla

A cewar hukumomin kasar filin wasannin na King Fahad zai iya daukar sama da mutum dubu 40 ko da kuwa an ware wuraren zama mata da maza daban-daban.

Saudi Arabia dai ita ce ja gaba a jerin kasashen duniyar da ke tsananta dokokin mata yayinda kuma ita ce kasa daya tilo da ta haramta tuki ga mata.

A ka’idar kasar dai Mahaifi ko miji ko kuma dan uwa Namiji ne ke shigewa mace gaba a harkokin da suka shafi Karatu ko tafiye-tafiye koma wasu al’amura da za su iya hada mu’amala tsakanin mace da namijin da ba muharraminta ba.

Sai dai ana ganin kasar yanzu tana sassautowa, la’akari da manufofin da take son cimmawa nan da shekara ta 2030.

A watan Yulin da ya gabata ne dai kasar ta amince da shigar da darussan wasanni ga mata a makarantunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.