Isa ga babban shafi
Myanmar

Sojin Myanmar sun bude wuta kan fararen hula

Sojin Myanmar sun bude huta kan fararen hula ‘yan kabilar Rohingya, mafi akasarinsu mata da kananan yara, yayinda suka yi yunkurin ketara kan iyakar kasar zuwa Bangladesh, don gujewa sabon tashin hankalin da ya barke a jihar Rakhine.

Wasu daga cikin dubban Musulmi 'yan kabilar Rohingya da sojin Myanmar suka budewa wuta, a lokacin da suka yi yunkurin ketara kan iyakar kasar zuwa Bangladesh a ranar 26 ga watan Agusta 2017.
Wasu daga cikin dubban Musulmi 'yan kabilar Rohingya da sojin Myanmar suka budewa wuta, a lokacin da suka yi yunkurin ketara kan iyakar kasar zuwa Bangladesh a ranar 26 ga watan Agusta 2017. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da ke kan iyakar Ghumdhum ta Bangladesh, ya rawaito ganin tarin kwanson alburusai na bindigogi masu sarrafa kansu, da sojin na Myanmar suka bude wuta da su kan yan kabilar ta Rohigya da suke kokarin ketara wani tsauni zuwa Bangladesh.

To sai dai zuwa yanzu babu alkalumman yawan wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata.

Dubban Musulmi ‘yan Kabilar Rohingya ne suka makale a kan iyakar Myanmar da Bangladesh, bayan sabon fadan daya barke tsakanin; 'yan tawayen kabilar da sojoji a jihari Rakhine ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ya haddasa mutuwar akalla mutane 92, ciki harda jami'an sojin kasar 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.