Korea ta Arewa ta sake harba makamai masu linzami
Kasar Korea ta Arewa ta sake harba makamai masu linzami zuwa gabar tekun da ke gabashinta, dai dai lokacin da sojin Amurka da na Korea ta Kudu ke gudanar da atasaye, wanda Korea ta Arewa ta bayyana shi a matsayin tsokanar yaki daga bangaren kasashen biyu.
Wallafawa ranar:
Sai dai cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Amurka, ta ce, Korea ta Arewan bata samu nasarar gwajin makamai masu linzamin uku ba, masu cin gajeren zango.
Makami na farko dai ya tarwatse ana harba shi, yayinda sauran guda biyun suka gaza yin nisan da ake bukata, inda sukai tafiyar kilomita 250 kawai zuwa cikin teku.
Amurka ta ce gwajin makaman bai yi wata barazana ga rundunar ta ba da ke tsibirin Guam, inda a farkon watan da muke ciki Korea ta Arewa ta yi barazanar kai wa hari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu