Isa ga babban shafi
Qatar

Mun mallaki arzikin dala biliyan 340 a asusun ajiya - Qatar

Gwamnatin kasar Qatar ta ce a halin yanzu fa ta mallaki zunzurutun kudi da ta dade da yin kawnciyar magirbi a kai, da yawansa ya kai dala biliyan 340, a matsayin rarar kudin da ta tanada don gaba.

Gwamnan babban bankin kasar Qatar Sheikh Abdullah bin Saoud al-Thani
Gwamnan babban bankin kasar Qatar Sheikh Abdullah bin Saoud al-Thani REUTERS/Hamad I Mohammed/File Photo
Talla

Yayin da yake sanar da haka, a wata zantawa da yayi da kafar yada labaran CBNC, Gwamnan babban bankin kasar ta Qatar, Shiekh Abdalla Bin Saoud al-Thani, ya ce babban bankin kasar kadai, ya mallaki arzikin dala biliyan 40 ciki harda tarin zinare, yayinda ita kuma gwamntin ta Qatar ta mallaki arzikin dala biliyan 300 a matsayin rara da ta adana a bitalmalinta.

Dan haka a cewar Shiekh Abdalla Bin Saoud al-Thani, matakin wariya ko yanke alaka da ita da kasashen Saudiya, Hadaddiyar daular Larabawa, Baharain da kuma Masar suka yi ba zai girgiza mata tattalin arziki ba kamar yadda suka bukata.

A makwannin da suka gabata, Saudiya da sauran kasashen larabawa da suka yanke alaka da ita, suka bai wa Qatar wasu jerin sharudda guda 13, daga ciki kuma akwai bukatar rufe gidan talabijin na Aljazeerah, yanke alaka da Iran da kuma rufe sansanin sojin Turkiya da ke kasar, wadanda suka ce dole da cikasu cikin kwanaki 10, kafin zama a teburin sulhu.

Sai dai Qatar din ta yi watsi da sharuddan, duk da karin wa'adin kwanaki biyu da kasashen larabawan suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.