Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula 100,000 sun makale a Raqa na Syria

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da fararen hula 100,000 ne suka makale a Raqa, a fadan da ake gwabzawa domin kwato yankin daga mayakan IS.

Tun a 2014 IS ta kwace Raqa
Tun a 2014 IS ta kwace Raqa AFP/WELAYAT RAQA/AFP/
Talla

Shugaban hukumar, Zeid Ra’ad Al Hussein ya bayyana damuwarsa ga makomar mutanen a Raqa da hare haren da ake kai wa IS ta sama ke rutsawa da su.

Akalla fararen hula 173 ne suka rasa rayukan su a hare haren jiragen sama da aka kai tun tun a farkon watan yuni. Hukumar tace adadin fararen hular da suka mutu na iya zarce haka.

Fararen hula da sukayi yunkurin tserewa na cikin hadarin rasa rayukan su sakamakon hare haren sama dake rutsawa da su.

Zeid ya ce a cikin sati 3 da suka gabata, hare-haren da mayakan IS suka kai a birnin raqa yayi sanadiyan barin fararen hula cikin fargaba da juyayin rashin sanin makomar su.

Adadin fararen hular da ke cikin mawuyacin hali na nuna cewa ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta bude wata sabuwar hanyar isar da kayyyakin jin-kai ga jama’ar Raqa da ke cikin mawuyacin hali.

Zeid ya yi kira ga bangarorin da ke yaki a Raqa su mutunta dokokin duniya wajen kare rayukan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.