Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

MDD ta nuna shakku kan Amurka game da rikicin Syria

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura, ya bayyana shakku kan matsayin sabuwar gwamnatin Amurka kan halin da ake ciki a kasar Syria.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura REUTERS/Pierre Albouy
Talla

De Mistura ya shaidawa mahalarta wani taron samar da tsaro da aka fara jiya lahadi a birnin Munich na kasar Jamus hakan, yayinda ake shirin komawa tattauna warware rikicin na Syria a birnin Geneva.

Jakadan na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi sanin matsayin Amurka kan tattaunawar, Inda ya ce a halin yanzu ba shi da masaniya, tare da zargin sabuwar gwamnatin Donald Trump da kokarin janyewa daga kokarin da kasashen duniya ke yi domin warware wannan rikici.

De Mistura ya ce a iya saninsa Amurka da manyan manufofi guda uku, da suka hada da fada da ayyukan ta’addancin kungiyar Daesh, hana wasu kasashen samun gidin zama a yankin da kuma cutar da wasu kasashen aminanta da ke wannan yanki.

Manzon na MDD bai ambaci sunan wata kasa a matsayin wadda ke neman yin kane-kane a cikin lamurran siyasar yankin na Gabas ta Tsakiya, to sai dai manazarta sun fahinci De Mistura na nufin Iran ne da kuma wadanda ke adawa da ita a rikicin, da suka hada da Saudiyya ko kuma Turkiyya.

Wani lokaci a baya, jakadan musamman na Amurka da ke sa-ido kan yakin da ake yi da kungiyar IS Brett McGurk, ya ce ko shakka babu gwamnatin Trump na nazari dangane da irin rawar da za ta taka a rikicin na Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.