Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

“Koriya ta Arewa ce ta sa aka kashe Kim Jong-Nam”

Koriya ta kudu ta ce Matan da suka kashe Kim Jong-Nam a Malaysia a ranar Litinin, jami’an Koriya ta Arewa ne da shugaban kasar Kim Jong-Un ya ba umurnin su kashe dan uwansa da suke uba guda.

Kim Jong-Nam da aka kashe a Malaysia
Kim Jong-Nam da aka kashe a Malaysia REUTERS/Eriko Sugita/File Photo
Talla

‘Yan Sanda a Malaysia sun sake kama wata mata da ake zargin tana da hannu wajen kisan Kim Jong-Nam a lokacin da ya ke shirin hawa jirgin sama a Kuala Lumpur.

Sanarwar ‘Yan Sandan tace an kama matar mai shekaru 28 da ke dauke da fasfo din Indonesia lokacin da take kokarin barin kasar.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Malaysia Tan Sri Noor Rashid Ibrahim ya ce suna sa ran kama wasu Karin mutane nan gaba kadan.

Koriya ta Arewa ba ta ce komi ba zuwa yanzu a game da kisan, amma jami’an diflomasiyarsa sun ziyarci inda ake binciken gawar Jong-Nam

Hukumomin Malaysia sun ce za su ba Koriya ta arewa gawar bayan sun kammala bincike.

Mata biyu ne ake zargin sun kashe Jong-Nam ta hanyar allura da sinadari mai guba wadanda rahotanni suka ce sun samu horo na musamman kan kisa a Koriya ta Arewa.

Kim Jong-Nam shi ya kamata ya zama shugaban Koriya ta Arewa a mastayin shi na babba a gidan tsohon shugaban kasar Kim Jong-Il da ya rasu a 2011 amma mulkin kasar ya fada hannun kanin shi Jong-Un bayan kama ya yi kokarin shiga Japan da fasfo na jabu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.