Isa ga babban shafi
Turkiya

'Yan sandan Turkiya sun kame mutane 450

‘Yan Sanda a kasar Turkiya sun sanar da kama mutane akalla 450 da ake zargin yan kungiyar ISIS ne a wani sumame da suka yi a fadin kasar.

'Yan sandan Turkiya
'Yan sandan Turkiya
Talla

Kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewar wannan shine samame mafi girma da Jami’an tsaron suka yi wanda ya kaiga kama mutane 448, cikin su harda baki yan kasashen waje.

'Yan Sandan sun kaddamar da samamen ne wata guda bayan wani kazamin harin da aka kai wani gidan rawa dake Istanbul wanda mayakan ISIS suka dauki alhakin kai harin.

Cikin wadanda jami’an tsaron suka kama akwai 'yan kasar Syria 150 da aka samu a otel otel da wasu gidajen dake garin Sanliurfa da kuma wasu 47 kusa da Gazientep.

'Yan Sandan sun ce an tsare wasu mutane 60 akasarin su yan kasashen waje a wasu yankuna 4 na birnin Ankara, yayin da aka kama wasu da dama a Bursa dake yammacin Antalya da kuma Bingol dake Yankin Gabas.

Kasar Turkiya na daga cikin kasashen dake fama da hare haren ta’addanci wadanda mayakan ISIS ko kuma na kungiyar Kurdawan PKK ke daukan alhaki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.