Al'ummar Korea ta Kudu na zanga-zanga
Shugabar kasar Korea ta kudu, Park Geun Hye, na fuskantar mastin lambar ta sauka daga mulki tun bayan wata badakalar rashawa da a yanzu ta haifar da gaggarumin gangami adawa da gwamnati a sassan kasar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga birnin Seoul sun ce masu gangami dauke da aluna sun hada da daliban makarantu da shugabanni Mujami’a da leburori da manoma da kanana yara da dai sauran su, duk sun fantsama kan tittuna kasar suna nuna fushinsu ga Shugabar.
Sama da mutane miliyan 1 aka rawaito sun fantsama kan tittuna kasar bayan bankado badakalar kan shugabar da ke yakin tsallake rigigimun siyasan da ya dabaibaiye ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu