Mayakan IS sun sace dubban mutane daga kauyukan Mosul
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mayakan IS sun sace dubban fararen hula wadanda ke zaune a kauyukan kusa da birnin Mosul.
Wallafawa ranar:
Majalisar ta kara da cewa, sakamakon kin biyayya gare su, mayakan na IS, sun yiwa wasu tsaffin jami’an tsaron Iraqi su 190 kisan gilla tare da wasu fararen hula 42.
A gefe guda kuma har yanzu dai sojin Iraqi da hadin gwiwar mayakan Kurdawa na cigaba da gwabza fada da mayakan na IS, a kokarinsu dannawa cikin birnin na Mosul.
Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargabar cewa, mayakan IS za suyi garkuwa da sauran fararen hula 1,500,000 da suka rage a cikin birnin Mosul, muddin aka dada matsar birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu