Isa ga babban shafi
Uzbekistan

Shugaban kasar Uzbekistan ya rasu

Shugaban kasar Uzbekistan, Islam Karimov ya rasu yana mai shekaru 78 bayan ya yi fama da shanyewar gefen jiki kamar yadda majiyoyin diflomasiya suka sanar a wannan jumma’a.

Marigayi  Islam Karimov na Uzbekistan
Marigayi Islam Karimov na Uzbekistan REUTERS/Maxim Shemetov/File Photo
Talla

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren gwamnatin Uzbekistan da ke tabbatar da mutuwar shugaban, wanda ya shafe kusan shekaru 30 yana jagorantar kasar mai yawan al’umma miliyan 32.

Sai dai rahotannin da suka fito daga kasar a safiyar wannan rana ta jumma’a, sun tabbatar da matsanacin rashin lafiya da shugaban ke fama da shi.

Ita ma gwamnatin Turkiya ta bakin Firaministsn kasar, Binali Yildrim, ta sanar da mutuwar shugaba Islam Karimov, yayin da ta mika sakon ta’aziya ga ilahirin al’ummar Uzbekistan mai makwabtaka da Afghanistan.

A lokacin da ya ke raye, marigayin ya sha caccaka daga kasashen Yamma da kungiyoyin kare hakkin dan Adam kan matakansa na murkushe gungun jama’a saboda ra'ayoyinsu da suka sha ban-ban da nasa.
 

Kazalika an zargi Karimov da gudanar da mulkin kama karya a kasar, wadda ta karbi ‘yanci daga Tarayyar Soviet a shekara ta 1991.

Kawo yanzu dai babu wani tsayayyen mutun da ake ganin zai maye gurbin Islam Karimov a matsayin sabon shugaban kasar ta Uzbekistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.