Isa ga babban shafi
Saudi

Hamza Bin Laden ya bukaci a kawar da gidan sarautar Saudiya

Dan Marigayi Osama Bin Laden wanda ya kafa kungiyar Al Qaeda ya yi kira ga al’ummar kasar Saudiya da su kawo karshen mulkin gidan sarautar Ali Sa’ud domin ‘yantar da kansu daga mamayar Amurka.

Hamza Ben Laden
Hamza Ben Laden AFP PHOTO/AL-JAZEERA
Talla

Hamza Bin Ladan ya yi kira ga matasa a kasar Saudiya da su shiga kungiyar Al Qaeda da ke kasar Yemen domin su koyi yadda ake fada da makamai, daga nan sai su koma Saudiya domin kawar da gidan sarauta daga karaga.

Hamza Bin Laden, dan shekaru 23 ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa daya fitar.

Kungiyar Al-Qaeda reshen Yemen wadda Amurka ke cewa tana dahatsarin gaske, tun shekara ta 2009 ta hade reshen Al-Qaeda da ke Saudiya.

Marigayi Osama Bin Laden dan kasar Saudiyya ne amma kuma tushensa kasar Yemen ne.

A shekara ta 2011 ne sojan Amurka suka kutsa kai kasar Pakistan suka kashe Osama Bin Laden bayan sun shefe kusan shekaru 10 suna farautarsa.

Jami’an tsaron Amurka na ganin Hamza shi ne dan lelen marigayi Osama Bin Laden wanda ake zargi da hannu wajen kulla harin da aka kai waAmurka da ake yi wa lakabi da harin 9/11.

Tun a shekara ta 1994 ne dai Hukumomin Saudiya suka kwace izinin zama dan kasar Saudiyya daga hannun Marigayi Osama Bin Laden a lokacin da ya furta la’antar gidan sarautar Saudiya da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.