Syria ta hanawa ‘Yan tawaye bude hanyar Aleppo
Rahotanni daga Syria sun ce dakarun gwamnatin Bashar Al Assad sun kashe ‘Yan tawaye akalla 29 a yayin da ‘Yan tawayen ke kokarin bude wata hanyar shigar masu da kaya a yankin Aleppo.
Wallafawa ranar:
Kungiyar da ke sa ido a rikicin na Syria tace ‘Yan tawayen da aka kashe sun kunshi na kungiyar mayakan Faylaq al Sham da na mayakan al Nusra mai alaka da Al Qaeda.
Sai dai babu wani cikakken bayani akan adadin sojojin gwamnati da aka kashe a fadan da aka gwabza a yankin na Aleppo a yau Lahadi.
Rahotanni sun ce farmakin na dakarun gwamnati ya haramtawa ‘Yan tawayen bude hanyar a Aleppo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu