Isa ga babban shafi
India

Kotu ta yi wa 'yan Hindu daurin rai da rai saboda Musulmai

Kotun India ta yanke wa wasu mutane 11 ‘yan kabilar Hindu hukuncin daurin rai da rai bayan ta same su da laifin kashe Musulmai guda 69 a jihar Gujurat shekaru 14 da suka gabata.

Kotun India ta yanke wa 'yan kabilar Hindu 11 hukuncin dauri rai da rai saboda samun su da laifin kashe Musulmai a jihar Gujurat
Kotun India ta yanke wa 'yan kabilar Hindu 11 hukuncin dauri rai da rai saboda samun su da laifin kashe Musulmai a jihar Gujurat REUTERS/Stringer
Talla

Kotun ta kuma yanke wa wasu mutane 12 hukuncin zama gidan yari har na tsawon shekaru bakwai yayin da mutun na karshe aka yanke masa daurin shekaru 10 saboda samun su da hannu a tarzomar da ta kai ga kashe Musulman a ranar 27 ga watan Fabrairun shekara ta 2002.

Kananan yara da mata na cikin wadanda aka hallaka a jihar ta Gujurat kuma an kashe su ne ta hanyar sassara su da kona su, abinda aka bayyana a matsayin mafi muni da ya auku a lokacin tarzomar wadda aka dauki tsawon mako guda ana yin ta.

Tarzomar dai ta barke ne bayan wasu ‘yan Hindu guda 59 sun rasa rayukansu a jirgin kasa saboda tashin gobara kuma a farko, an zargi Musulmai da haddasa wutar gobarar.

Wannan ne ya sa ‘yan kabilar ta Hindu suka tayar da rikicin da ya yi sanadiyar mutane fiye da dubu 1, yawancinsu Musulmai.

Wata Musulma mai suna Zakia Jafri da aka kashe mijinta a tarzomar ta ce, hukuncin da kotun ta yanke ya yi sassauci sosai.

Suma masu shigar da kara sun bukaci a yanke wa daukacin mutanen da aka samu da aikata laifin hukuncin kisa saboda sun kashe Musulman da basu ji basu gani ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.