Isa ga babban shafi
Koriya ta kudu

Ana fargaban karancin naman kare a Koriya

Masu sana’ar kiwon karnuka a Koriya ta Kudu sun gabatar da kokon baransu ga hukumomin kasar domin gudun kada a sami karancin naman karnuka wanda mutanen kasar ke matukar bukata don ci.

Naman kare na daga cikin abinda aka fi yin kalaci da shi a Koriya ta Kudu
Naman kare na daga cikin abinda aka fi yin kalaci da shi a Koriya ta Kudu 路透社
Talla

Ofishin ma su kididdiga a Koriya ta Kudu sun ce, a duk shekara ana cin karnuka da yawansu suka haura tsakanin miliyan daya da rabi zuwa miliyan biyu da rabi, amma kuma masu kiwon karnukan na cewa, ana matukar karancin karnukan a yanzu.

Baya ga rashin tallafa masu, babban dalili da masu sana'ar kiwon karnukan ke ganin cewa shi ne ya haifar da karancin karnukan shi ne, wasu matasa na wannan zamanin ba sa sha'awar cin naman kare, don sun sami wasu abubuwan daban da suke kalaci da shi.

Gong In-Young, wani fitaccen mai sana’ar kiwon karnuka don ci ya ce, tilas tasa ya ya yi gwanjon karnuka 200  da ya samo daga kasashe daban-daban, duk dai saboda rashin kasuwar masu sha'awan cin karnukan.

Gong In-Young wanda shi ne na biyar wajen kasaita da arziki saboda sana'ar ya ce, ya ma riga ya bar sana'ar a yanzu, kuma har ya auna karnuka zuwa wasu kasashen duniya masu sha'awa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.