Isa ga babban shafi
UN-Syria

Manyan kasashen duniya na amfani da rikicin Syria wajen gwada karfin su

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon a karon farko ya zargi manyan kasashen duniya da amfani da rikicin Syria wajen gwada karfin su. 

Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon.
Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon. REUTERS/Adrees Latif
Talla

A sanarwar da yayi na cika shekaru biyar da fara yakin kasar, Ban ya ce inda manyan kasashen duniya sun hada kan su da an magance rikicin.

A wani mataki da ake ganin na ba sa bamba, Ban Ki Moon ya fito karara inda yake sukar manyan kasahsen duniya kan rawar da suka taka na jefa Syria cikin yaki saboda biyan bukatar kan su.

Duk da ya ke Sakatare Janar din bai ambaci sunan wata kasa ba, yace inda manyan kasashen dake Yankin da duniya baki daya sun hada kai da an kaucewa yakin da ake yanzu haka.

Ban ya bukaci samun nasarar tattaunawar da ake yi yanzu haka dan kawo karshen rikicin, inda yake cewar rashin samun nasarar taron ba zai yiwa mutanen Syria da al’ummar duniya alkhairi ba.

A karon farko, hadin kan wadanan kasashe 5 dake da kujerar din din din a Majalisar Dinkin Duniya ya haifar da ci gaban diflomasiya wajen tsagaita wuta da fara tattaunawa tsakanin bangarorin dake rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.