Isa ga babban shafi
Sri lanka

Sri Lanka ta fada cikin duhu irinsa na farko a shekaru 20

A karon farko a cikin shekaru 20 kasar Sri Lanka ta fada cikin duhu sakamakon katsewar wutar lantarki wanda ya haifar da karancin ruwan sha, katsewar sufuri da kuma kasuwanci a fadin kasar.  

Shugaban kasar Sri Lanka's Maithripala Sirisena
Shugaban kasar Sri Lanka's Maithripala Sirisena REUTERS/Dinuka Liyanawatte
Talla

Rahotanni sun ce haka kawai wutar ta katse jiya da rana, kuma kokarin mayar da ita ya ci tura har sai bayan sa’oi 7 kafin wasu sassan kasar suka samu wutar.

Shugaban hukumar samar da wutar lantarkin kasar Anura Wijepala ya dauki alhakin matsalar da aka samu inda ya ce zai sauka daga mukamin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.