Erdogan ya soki Amurka kan rikicin gabas ta tsakiya
Shugaban Turkiyya Raceep Tayyib Erdogan ya zargi Amurka da laifin haddasa rikice rikicen zub da jinin da ake a yankin gabas ta tsakiya, sakamakon gaza aiyana kungiyar Kurdawan Syria a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cewar shugaban na Turkiya matukar Amurka za ta cigaba da jan kungiyoyin kurdawa a jiki to fa babu shakka da hannun ta a zub da jinin da ake a yankin.
Ko a jiya talata ma sai da Turkiyan ta gayyaci jakadan Amurka a kasar don yimata Karin haske kan kalaman mai Magana da yawun gwamnatin Obama na cewa basa ganin kungiyoyin kurdawa a matsayin na ‘yan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu