Kotun India ta wanke Salman Khan daga laifin kisa
Babbar kotun kasar India ta wanke shahararren mai shirin Fim na India Salman Khan daga laifin kashe wani mutum ta hanyar take shi da mota sannan ya tsare a shekara ta 2002.
Wallafawa ranar:
Kotun wadda ta ke birnin Bombay ta wanke Khan mai shekaru 49 daga dukkanin tuhume tuhumen da ake yi masa bayan ya daukaka kara a gabanta.
Babbar Kotun ta yi watsi da hukuncin da wata karamar kotu ta yanke a baya, inda ta yanke wa Salman Khan daurin shekaru biyar a gidan yari bayan ta same shi da laifin kisan kai.
Tuni dai Khan ya fashe da kukan farin ciki bayan an wanke shi yayin da magoya bayansa da suka halarci farfajiyar kotun suka bige da murna.
Salman Khan dai ya kashe mutumin ne da motarsa kirar Land Cruiser bayan ya bi ta kan wasu mutane da ke kwana a titi da daddare a birnin Mumbai kuma rahotanni sun ce, sai da ya dirki barasa a gidan giya kafin ya tuka motar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu