Switzerland
Switzerland za ta karbi 'Yan gudun hijirar Syria 1,500
Kasar Switzerland tace za ta karbi yan gudun hijirar Syria 1500 a cikin shekaru biyu masu zuwa kana kuma zata kara yawan tallafin da take baiwa kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Sai dai gwamnatin kasar tace ba zata karbi yan gudun hijirar da yanzu ke kasashen Italia da Girka da aka riga aka yiwa rajista ba.
Switzerland ta ce ta ware Karin Dala miliyan 70 dan mikawa kasashen Syria, Iraqi da arewacin Afirka.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da baki ‘Yan gudun hijira ke ci gaba da kwarara zuwa Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu