Isa ga babban shafi
Afghanistan

Hare haren kasar Afghanistan sun sake yin sanadiyyar mutuwar jama'a

Yau Asabar an sake tabbatar da mutuwar wasu mutane 8, da hare haren birnin Kabul na kasar Afghanistan ya rutsa dasu.Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 44, wasu daruruwa suka sami raunuka, sakamakon hare haren kunar bakin waken da aka kai a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan. 

Wasu mayakan Taliban
Wasu mayakan Taliban AFP PHOTO / Noorullah Shirzada
Talla

Wadannan ne hare haren farkon da aka kai a birin Kabul, tun bayan sanarwar mutuwar tsohon shugaban kungiyar Taliban Mullah Omar, cikin makon da ya gabata.
Hare haren na jiya juma’a sun lalata gine da dama, yayinda suka haifar da cinkoso a asibitoci, inda aka yi ta kai gawarwaki da marasa lafiya.
Hare haren suna daga wadanda suka fi muni a birnin, tun bayan da aka kawo karshen aikin dakarun kungiyar tsaro ta NATO, cikin watan Disamban bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.