Isa ga babban shafi
China-India

Yawan al’ummar India za su haura China kafin shekarar 2022-Rahoto

A wani sabon Rahotan da ta fitar Majalisar dinkin duniya ta yi gargadi samun karuwar yawan alkallumar al’ummah a India sama da na china kafin shekarar 2022, adadin da ta ce  babba barazanar ce ga cigaban kasar.

REUTERS/Amit Dave
Talla

Sashen da ke bincike da kuma Nazarin kan yawan al’ummah a duniya na Majalisar dinkin duniya na cewa, a yanzu yawan al’ummar kasar india ya haura biliyan 1, alkallumar da ke tabbatar da cewa na bada jimawa ba kasar za ta haura China da ke da yawan Jama’a sama da biliyan 1.3 adadi mafi yawa a duniya.

Rahotan ya kuma bayyana cewa, matakin da China ta dauka na haramta haihuwa sama da guda ya taimaka mata matuka wajen takaita yawan al’ummar ta.

Rahotan dai ya cigaba da cewa, idan har aka ci gaba da samun karuwan yawan mutane a India ba tare da dauka wani matakin ba irin na China, to babu shaka kasar za ta fuskanci babban kalubali wajen samun ci gaba, karuwar talauci da yunwa, da kuma koma baya a fanin kiwon lafiya.

Har illa yau rahotan ya kuma bayyana cewa, itama kasar Najeriya da ke da yawan mutane  sama da miliyan 178 a yanzu na kan hanyar samun karuwar adadin jama’a da sama da kasar Amurka kafin shekarar ta 2050, inda akwai yiwuwar ta kasance kasa ta uku a duniya mafi yawan mutane.

Rahotanin dai na cewa yawanci an fi samun karuwar adadin mutane a kasashen da ke tasowa, musamma yankin Afrika.

Lamarin da masana su ka yi hasashen cewa kafin shekaru 35 masu zuwa, sama da rabin yawan alkallumar al’ummar duniya za su fi yawa a yankin Africa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.