Isa ga babban shafi
Iran

Khamenei ya gargadi Rouhani akan manyan kasashen duniya

Jagoran Addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gargadi shugaban kasar Hassan Rouhani akan sai ya yi taka-tsantsan da wasu manyan kasashen duniya domin a cewarsa ba abin yarda ba ne ga yarjejeniyar da suka amince ta Nukiliya.

Jagoran addini Ali Khamenei da Shugaba Rohan
Jagoran addini Ali Khamenei da Shugaba Rohan مهر
Talla

A cikin wata wasika da ya aikawa Rouhani, Khamenei ya bukaci shugaban ya sa ido sosai domin ana iya sabawa yarjejeniyar da suka amince kan shirin nukiliyan kasar.

A cikin wasikar, Khamenei ya taya Iran murnar nasarar cim ma yarjejeniya tsakaninta da manyan kasashen duniya shida da suka hada da Amurka da Faransa da Birtaniya da Rasha da China da kuma Jamus.

Khamenei ya ce cikin kasashen shida akwai wadanda ba abin yadda ba ne, amma ba tare da  zayyana sunayen kasashen da ya ke nufi ba.

Amma tsawon lokacin da aka shafe ana tattaunawa kan shirin nukiliyan Iran, shugaba Khemenei ya dade yana bayyana shakku akan Amurka da ke amintaka da Isra’ila.

Isra’ila dai ta fito a fili tana bayyana adawa da yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka amince da Iran.

Manyan kasashen dai na son Iran ta jingine shirinta na mallakar Makaman Nukiliya, kafin su janye takunkuman da suka kakaba ma ta.

Kuma a yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince, manyan kasashen duniyar za su janye takunkuman ne a sannu a hankali har Iran ta lalata shirinta na nukiliya.

Jerin Takunkuman dai sun shafi tattalin arzikin Iran.

Yanzu haka kuma kasashen Turai na rige rigen kulla huldar jakadanci da Iran da suke ake shirin janye wa takunkumin kariyar tattalin arziki bayan nasara kulla yarjejeniyar nukiliyar kasar.

Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce Birtaniya za ta bude ofishin Jakadancin ta a Tehran.

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus ya ce zai jagoranci tawagar ‘yan kasuwa zuwa kasar, yayin da Sakataren harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce nan gaba kadan zai ziyarci Tehran domin inganta hulda da Faransa.

A nasa bangaren shugaban Kasar Amurka barack Obama ya bayyana fatarsa na ganin kasar Iran ta sauya yadda ta ke tafiyar da al’amurranta bayan kulla yarjejeniyar nukiliyar da ta yi da sauran manayan kasahsen duniya.

Yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a fadarsa, Obama ya ce za su cigaba da kokarin tallafawa kasar wajen daukan matakan da suka dace duk da ya ke ba su da sahihanci akai.

Obama ya kuma ce ba za su mayar da huldar jakadanci da Iran ba kamar yadda suka yi da kasar Cuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.