Isa ga babban shafi
Indonesia-Malaysia

An gano Jirgin AirAsia a tekun Indonesia

Bisa dukkan alamu an kammala aikin neman jirgin AirAsia a yau Talata wanda ya bata dauke da mutasne 162 bayan masu aikin bincike sun tsinci takarcen jirgin da gawawwakin mutane da dama a cikin tekun Indonesia.

'Yan uwan Fasinjan jirgin AirAsia suna kuka bayan ganin hoton mutum a teku
'Yan uwan Fasinjan jirgin AirAsia suna kuka bayan ganin hoton mutum a teku REUTERS/Beawiharta
Talla

Alamu sun tabbatar da cewa Jirgin ya yi hatsari ne a tekun Java, kudu maso yammacin tsibirin Borneo, bayan ganin tarkacen jirgin da gawawwakin mutane da dama.

‘Yan uwan Fasinjan da ke jirgin sun rungume juna tare da zubar da hawaye a Surabaya a lokacin da suke kallon kafar Telebijin da ke nuna hoton gawa kwance a ruwa.

Mahukuntan Indonesia sun ce sun tsamo sama da gawar mutane 40 a cikin teku, yayin da ake ci gaba da aikin tsamo sauran gawawwakin a ruwa.
 

Tun da safiyar Talata ne Jami’an kasar Indonesia  suka ce sun hangi abubuwa da dama masu kama da tarkacen Jirgin mai lamba 8501.

Ma su aikin binciken sun ce abubuwan da suka hanga sun yi kama da kofar Jirgi da rigar ruwa a cikin teku.

Rundunar Sojin ruwan kasar Indonesia sun ce sun hango tarkacen jirgi masu girma guda 10 da wasu kanana da dama.

A ranar Lahadi ne Jirgin na AirAsia mai lamba 8501 ya bata dauke da mutane 162, yawancinsu ‘yan kasar Indonesia.

Kamfanin Jirgin kuma yace an samu matsalar sadarwa ne da matuka jirgin bayan ya tashi daga Surabaya zuwa Singapore.

Kasashen Australia da Malaysia da Singapore da kuma Amurka da Faransa suka shiga aiki neman jirgin a tekun Java, inda kasar Indonesia ke jagoranta, yayin da dangin mutane da ke cikin jirgin ke cikin halin dimauta, saboda rashin sanin halin da fasinjojin jirgin 162 ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.