Isa ga babban shafi
Saudiya

Dogaro da fetir hatsari ne

Daya daga cikin ‘ya’yan gidan sarautar Saudi Arabiya kuma attajiri Yarima Alwaleed bin Talal yace ci gaba da dogaro da kasar ke yi kan arzikin mai wani babban hatsari bayan faduwar farashin man zuwa kasa da dala 80. Alwaleed yace faduwar farashin man ya tababtar da shawarar da suka bai wa gwamnatin kasar cewar ta nemi wasu hanyoyin samun kudaden shiga sabanin dogaro da fetur.

Sarki Abdallah na Saudiya da Ministan harkokin wajen kasar Saud al-Faisal da Attajiri dan gidan Yarima Alwaleed bin Talal
Sarki Abdallah na Saudiya da Ministan harkokin wajen kasar Saud al-Faisal da Attajiri dan gidan Yarima Alwaleed bin Talal Forbes
Talla

Kashi 90 na kudaden shiga da Saudi Arabiya ke samu na zuwa ne daga cinikin man fetur. Alwaleed ya shaidawa manema labarai cewa wannan matsala ce mai hatsari ga tattalin arzikin Saudiya a nan gaba.

Alwaleed yana cikin manyan attajiran duniya.

An samu faduwar farashin mai ne bayan da Saudiya ta bayyana rage farashin da ta ke sayarwa Amurka.

Tun da farko dai Shugabar Asusun bayar da lamuni ta duniya Chritine Lagerde ta yi gargadin cewa kasashen larabawa na iya fuskantar matsala a kasafin kudinsu idan aka samu faduwar fashin Mai a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.