Isa ga babban shafi
India

India ta haramta yin ba-haya a daji

A wani mataki na tsabtace muhalli, gwamnatin kasar India tace zata ba kananan yara mabusa domin su dinga tona asirin mutanen da ke fita filin Allah suna ba-haya. Tuntube da ba-haya dai matsala ce a indiya, akan haka ne Firaministan kasar ya bukaci al’ummar kasar su tanadi makewayi nan da shekaru hudu masu zuwa, a matakan da gwamnatinsa ke dauka na tsabtace muhalli.

Zanen wani yana ba-haya a daji
Zanen wani yana ba-haya a daji fpnotebook.com
Talla

Dabarar amfani da mabusar ga yara shi ne don kunyata mutanen da ke ba-haya a sarari maimakon ban-daki. Kuma wasu gwamnatocin Jihohin Indiya sun ce zasu gaggauta kaddamar da sabon shirin na tsabtace muhalli.

A karkashin tsarin kuma za’a ilmantar da yara yadda zasu kula da tsabtace muhalli, kafin ba su mabusar da zasu zama masu gadin muhallinsu.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace kusan kashi 50 na mutanen India suna ba-haya ne a sararin Allah sabanin ban-daki.

Amma yawanci mata ne suka fi amfani da ban-dakin, saboda gudun tabi’ar fyade da ta zama babbar matsala a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.