Isa ga babban shafi

Mayakan IS sun sako 'yan Turkiyya da suka yi garkuwa dasu a Iraqi

Hukumomin kasar Turkiyya sun ce an sako ‘yan kasar su 49, da ‘yan kungiyar IS suka yi garkuwa dasu a arewacin kasar Iraqi, fiye da watanni 3 da suka gabata. Fraiministan kasar ta Turkiyya Ahmet Davutoglu yace yau Asabar da safe aka dawo da dukkan mutanen gida, inda yace duk suna cikin koshin lafiya.A ranar 11 ga watan Yuni, mayakan kungiyar ta IS suka yi awon gaba da mutanen, da suka hada da jami’an diplomasiyya, yara kanana da dakarun musamman a birnin Mosul na arewacin kasar ta Iraqi. 

Fraiministan kasar Turkiyya, Ahmet Davutoglu
Fraiministan kasar Turkiyya, Ahmet Davutoglu Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.