Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Sabon shirin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas

Isra’ila da Hamas sun amince da wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’oi 72 a tsakaninsu, bayan da Israila ta ce ta yi nasara rusa dukkanin hanyoyin karkashin kasa da Hamas ke amfani da su wajen kai ma ta hari.

Sojojin Isra'ila a Gaza Agusta 2014
Sojojin Isra'ila a Gaza Agusta 2014 REUTERS/Baz Ratner
Talla

Har ila yau Isra’ila ta ce za ta janje dakarunta da suka share tsawon kwanaki 28 suna barin wuta a kan Gaza.

Osama Hamdan, daya daga cikin shugabannin Hamas ya ce sun amince da yarjejejiyar, to sai dai suna fatar Isra’ilan za ta aiwatar da ita a zahiri sannan kuma a kawo karshe killacewar da aka yi wa Gaza.

Shi kuwa mai Magana da yawun gwamnatin Isra’ila Mark Ragev cewa yana da muhimmanci Hamas ta yi bayani kan dailinta na kin amincewa da wannan yarjejeniya makwanni uku da suka wuce, sai bayan da aka kashe mutane da dama sannan ta amince da haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.