Isa ga babban shafi
isra'ila-Falesdinu

Isra'ila ta shelanta tsagaita wuta na sa'o'i 7

Rundunar tsaron Isra’ila ta sanar da tsagaita wuta a kan yankin Gaza na tsawon sa’o’i 7 a yau litinin domin bai wa jami’an agaji isar da kayayyakin jinkain ga dubban mutanen da ke cikin mawuyacin hali a yankin.

Harin Isra'ila a wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya
Harin Isra'ila a wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

To sai dai kungiyar Hamas wadda ke iko da zirin da Gaza, ta ce ba ta da tabbas idan har wannan shiri zai kai ga samu nasara, inda ta gargadi mazauna yankin da su yi takatsantsa.

Isra’ila dai ta ce shirin tsagaita wutar zai yi aiki ne a duk fadin yakin na Gaza mai mutane sama da milyan daya da dubu 700, to sai dai shirin bai shafi birnin Rafah da zagayensa ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Isra’ila da Hamas ke sanar da tsagaita wuta domin bayar da damar isar da kayayyakin jinkai ba to amma sai a wayi gari shirin ya wargaje. Kawo yanzu dai hare-haren na Yahudawa a kan Falasdinawa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 1 da 800 a cikin kwanaki 28.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.