Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Shirin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas ya rushe

Shirin tsagaita wuta da aka sanar domin bayar da damar isar da kayayyakin agaji ga jama’ar yankin Gaza, ya rushe ne bayan sa’o’I uku da soma yin aiki da shi, inda Isra’ilan ta yi zargin cewa Hamas ke da laifin yin hakan tare da kama wani soja daya na Isra’ila a kusa da mashigin Rafah.

Garin Rafah a ranar 1 ga watan Agustan 2014
Garin Rafah a ranar 1 ga watan Agustan 2014 AFP PHOTO/ SAID KHATIB
Talla

Isra’ilan dai ta mayar da martani da zafafen hare-hare ta sama, inda rahotanni ke cewa a yau juma’a kawai ta kashe fiye da Falasdinawa 70.

A dazun nan kuwa, mataimakin mai bai wa shugaban Amurka Barack Obama shawara kan lamurran tsaro Tony Blinken, ya fito ya yi kakkausar suka ga kungiyar Hamas, inda ya dora alhakin kisan da Isra’ilan ke yi wa Palasdinawa akan kungiyar.

To sai dai yayin da adadin Faladinawa da Isra’ilan ta kashe ya haura dubu daya da dari biya, a yau juma’a sarki Abdullah na kasar Saudiyya ya yi wata fitowar ba zata, inda ya yi kakkausar suka ga abinda ya kira shirun kasashen duniya kan yadda Isra’ilan ke kashe al’ummar Palasdinu, to sai dai Sarkin bai bayyana abinda za su a nasu bangare domin kawo karshen hakan ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.